
An tashi daga wasa kowacce ƙungiya na da ci daya tsakanin Enyimba da Heartland, yayin da a Katsinan Dikko, Plateau United tayi rashin nasara a hannun Katsina United da ci daya da nema, Niger Tornadoes ta doke Kwara United da ci biyu da daya, aka kuma tashi daga wasa kowacce ƙungiya na da ci biyu tsakanin Rivers United da Bendel Insurance.
Zuwan yanzu Remo Stars ita ce akan gaba da yawan maki 42, yayin da Shooting Stars ta koma kan matsayi na biyu da maki 36, sai Rivers United a matsayi na uku da maki 35, yayin da El-Kanemi Warriors ke a matsayi na hudu da maki 32.
Kungiyoyin da ke matsayi na hudun karshe sun hada da Bendel Insurance a matsayi na 17 da maki 22, sai Lobi Stars a matsayi na 18 da maki 21 yayin da Akwa United ke a matsayi na 18 da maki 20, sai Nasarawa United a matsayi na 20 da maki 19.
Za’a fara gabatar da wasannin mako na 22 na gasar a ranar Asabar, a inda Remo Stars ke ziyartar garin Akure domin karawa da Sunshine Stars, sai kuma Bendel Insurance da zata karbi bakuncin Katsina United.









