CBN yayi kari akan haraji cirar kuɗi a na’urar ATM

Babban bankin Najeriya CBN yayi kari akan harajin da ake karba wajen masu amfani da na’urar ATM a yayin cirar kuɗi.
A wata sanarwar da Babban Bankin ya fitar mai ɗauke da kwanan watan goma ga watan Fabrairu shekara ta 2025, ya bayyana cewa sauyin da aka samu ya shafi dukkanin bankuna kuma zai fara aiki ne a ranar daya ga watan Maris na wannan shekarar.
Sanarwar wacce ke ɗauke da sa hannun mai rikon muƙamin daraktan al’amurran kuɗi na bankin, John S. Onojah,ya bayyana cewa daga yanzu dukkanin mai ajiya a banki da ya cire kuɗi da yawan su ya kai N20,000 a na’urar ATM na bankin da ba nasa ba, kuma a wajen harabar banki, zai biya haraji Naira dari biyu N200.
Yayin da wanda ya cire N20,000 a na’urar ATM dake harabar bankin da ba a shi ya ke ajiya ba, zai biya Naira dari N100 a matsayi caji.
Sai dai kuma sanarwar ta bayyana cewar babu haraji akan cirar kuɗi a na’urar ATM mallakin bankuna da mutum ya ke ajiya kamar yadda lamarin ya ke a baya.









