
A gobe Asabar za’a fara gabatar da wasannin mako na 20 na gasar firimiya lig ta kasa bayan hutun makonni uku.
A wasannin da za’a gabatar a ranar Asabar Nasarawa United za ta karbi bakuncin Katsina United, Bayelsa za ta ziyarci Abia Warriors, Enugu Rangers na gida ita da Niger Tornadoes, Sunshine Stars za ta fafata da Ikorodu City.
Sai kuma rana Lahadi, a inda Remo Stars za ta ziyarci Akwa United, Heartland za ta karbi bakuncin Lobi Stars sai kuma wasa tsakanin Plateau United da Rivers United.
Hukumar shirya gasar ta NPLF ta sauya ranakun da za’a gabatar da wasu wasanni zuwa wani lokaci da za’a sanar anan gaba, wasannin da aka sauya wa rana sun hada da wasan da Kano Pillars za ta karbi bakuncin Ek-Kaneni Warriours da wasan Kwara United da Shooting Stars da kuna wasa tsakanin Bendel Insurance da Enyimba.
Zuwa wannan lokaci dai, Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Remo Stars ita ce a kan gaba a gasar da yawan maki 36 daga wasanni 19. Yayin da Rivers United ke biye ma ta baya da maki 34, sai kuma Shooting Stars Ibadan a matsayi na uku da maki 33, yayin da Rangers International ke a matsayi na hudu da maki 31.
Ƙungiyoyin da ke matakin karshe na gasar sun hada da Plateau United a matsayi na 17 da maki 20, sai Lobi Stars a matsayi na 18 ita ma dai da maki 20 yayin da Akwa United ke a matsayi na 19 da maki 19 sai Kuma Nasarawa United wacce ke kan matsayi na 20 kuma na karshe da maki 16.









