Anyi kira ga gwamnatin tarayya da ta karfafa shirin ta na tallafawa manoma

Shugaban bankin raya kasashen nahiyar Afrika,
(AfDB), Dr. Akinwumi Adesina yayi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta kara himma bisa kokarin ta na tallafawa manoma domin kawo karshen karancin abinci da kuma tsadar sa a Najeriya.
Dr. Adesina yayi kiran ne a yayin bikin kaddamar da masana’antar sarrafa waken-suya da aka samar a yankin Gora dake karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.
Shugaban bankin na raya kasashen nahiyar Afrika ya bayyana damuwa da yadda farashin kayan abinci ke cigaba da tashin a kasuwanni tare da yin kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan karfafa manufofin ta na samar da abinci musamman ma wadanda zasu karfafa gwiwar manoma tare da tallafa musu domin shawo kan lamarin cikin gaggawa.
Da ya juya kan masana’antar sarrafa waken-suya da ya kaddamar, Dr Adesina ya bayyana cewa samar da masana’antar zai iya samar da lita dubu goma na man awo, waken-suya a kowacce rana, lamarin da ya ce zai kawo karshen shigo da man na waken-suya cikin kasar nan.









