LabaraiWasanni

An kwantar da Mbappe a asibiti

An kwantar da ɗanwasan gaba na Real Madrid Kylian Mbappe a asibiti sakamakon rashin lafiyar da ta hana shi buga wasan farko a gasar kofin duniya ta Club World Cup da Al Hilal ranar Laraba.

Mbappe mai shekara 26 bai yi atasaye ba a ranar Talata saboda zazzaɓi.

Real Madrid ta bayyana a yau Alhamis cewa ana yi wa ɗanwasan na Faransa gwaje-gwaje da dama bayan ya yi ƙorafin fama da ciwon ciki.

Wasan na Real da Al Hilal a Rukunin H ya tashi canjaras 1-1 kuma sai a ranar Lahadi za ta kara da Pachuca ta ƙasar Mexico a wasa na biyu na zagayen cikin rukuni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button