KasuwanciLabaraiTattalin Arziki
NNPCL ya kara rage kuɗin Man fetur.

A karo na biyu cikin mako guda, Kamfanin Man fetur na Najeriya NNPCL ya sanar da kara rage kuɗin litar man fetur.
Kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito, a yanzu NNPCL na sayar da lita ɗaya na man fetur akan Naira 890 a maimakon Naira 895 da ake sayarwa a baya, abinda ke nuni da cewar an samu ragin Naira 5 akan farashin da ake sayar da litar man a baya.
Rahotannin sun bayyana cewa da dama daga cikin gidajen sayar da man fetur dake babban birnin tarayya Abuja suna amfani da sabon farashin wajen sayarwa da masu bukatar man fetur.
Sai dai kuma rohoton ya bayyana cewa gidajen man da ke sayar da man Dangote, na sayar da man ne akan Naira 885.









