
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido ya shawarci Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi da su nemi gafarar al’ummar Najeriya bisa goyon bayan da suka bawa Jam’iyyar APC a zaɓen shekara ta 2023.
Alhaji Sule Lamido wanda ya bayyana haka a yayin wata hirar da yayi da gidan telebijin na Arise, ya kuma kalubalance yan siyasan biyu kan yaudarar yan Najeriya wajen tallata takarar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, yana mai cewa duk da cewar jam’iyyar PDP ce tayi wa Amaechi da El-Rufai gata irin na siyasa, sai gashi sun taka rawa wajen durƙusar da jam’iyyar.
A don haka Alhaji Sule yayi kira ga yan siyasan biyu da su fito fili su nemi gafarar yan Najeriya, ganin cewar sun taka rawa wajen jefa ƙasar cikin halin da ta samun kanta.









