
Tarihi na neman maimaita kan sa, musamman ma akan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, duba da cewa a irin wannan lokacin ne, na farko shekara a kowacce kakar wasanni ƙungiyar ke samun kuma baya a kokarin ta na ganin ta lashe gasar firimiya lig.
A wasan da ta fafata a ranar Asabar tsakanin ta da kungiyar Brighton, duk da cewa arsenal ita ce ta fara zura ƙwallo a raga, ta hannun matashin ɗan wasan ta mai shekaru 17 da haihuwa, ɗan asalin Najeriya, Ethan Nwaneri, rama ƙwallon da Brighton tayi a zango na biyu na wasan da alama ya rage kwarin gwiwar da magoya bayan ƙungiyar ke dashi na lashe gasar firimiya lig a bana, kuma a yanzu haka kungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool wacce ke jan ragamar gasar ta bawa Arsenal ɗin tazarar maki biyar, duk da cewar akwai banbanci wasannin biyu a tsakanin su.
Yanzu dai hankalin kocin Arsenal, Mikel Carter’s zai kuma ga zagaye farko na wasan kusa dana karshe na gasar Carabao Cup da ƙungiyar za ta fafata da Newcastle a ranar Talata 7 ga watan Janairu da kuma wasan mako na 21 na gasar firimiya lig da zasu kara da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham a ranar Laraba 15 ga watan Janairu.
Wasannin biyu dai za suyi tasiri wajen fayyace makomar ƙungiyar a ƙarshen kakar wasannin da muke ciki.
Shin ku na ganin Arsenal za ta lashe gasar firimiya lig a bana? Za ku iya bayyana mana ra’ayin ku a “comment section” na wannan labarin.









