Tsadar Abinci: Gwamnonin Najeriya sun sha alwashin samar da kyakkyawar yanayin kasuwanci.

Gwamnonin Najeriya 36, sun bayyana aniyarsu na samar da kyakkyawar yanayin kasuwanci ta hanyar saukaka haraji kamar yadda yake ƙunshi a cikin sabuwar dokar haraji ta kasa dake jiran amincewar shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu.
Wannan dai na daya daga cikin matsayar da gwamnonin suka cimma a yayin taron su da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.
Da yake karin haske akan sakamakon taron, gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa gwamnonin sun kuma amince su cire duk wani shinge bincike na ababan hawa, waɗanda aka samar ba bisa ka’ida ba akan manyan titunan jihohin su domin samar da kyakkyawar yanayin zirga-zirga ababan da kuma kasuwanci.
Taron gwamnonin na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi da kuma matsalolin tsaro a Najeriya.









