LabaraiWasanni

NFF za ta gabatarwa da yan Najeriya sabon kocin Super Eagles.

A gobe Litinin, hukumar ƙwallo ƙafa ta kasa za ta gabatar da sabon mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, Éric Chelle.

A wata sanarwar da daraktan sadarwa na hukumar ƙwallo ƙafa ta kasa NFF, Ademola Olajire, ya fitar ta bayyana cewa za’a gudanar da bikin gabatarwar ne a filin wasa na Moshood Abiola da ke babban birnin tarayya Abuja da misalin karfe 11 na rana.

Da yake karin haske akan naɗin Eric Chelle a matsayin sabon mai horar da ƙungiyar Super Eagles, shugaban hukumar ƙwallo ƙafa ta kasa, Ibrahim Gusau, ya bayyana gamsuwa da kwarewar da sabon mai horar wa ke dashi tare da karfin gwiwar cewa ko shakka babu zai bawa maraɗa kunya.

Ana sa ran, a taron na gobe hukumar za ta bayyana sunayen waɗanda zasu taimakawa sabon mai horarwar wanda babban aikin da ya ke gaban su shine wasannin sharar fagen neman kaiwa ga shiga gasar cin kofin duniya da Super Eagles din za ta fafata da Rwanda da kuma Zimbabwe a watan Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button