KasuwanciLabaraiTattalin Arziki

Sabuwar dokar haraji za ta fara aiki a watan Yuli

Shugaban kwamitin gyare-gyaren haraji ta Najeriya, Taiwo Oyedele, ya ce ƙudurin haraji da ke gaban majalisar ƙasar zai zama doka kafin rubu’in farko na shekarar nan ta 2025 na ƙare.

Dokar dai ta ɗauki hankalin mutane ƙasar, lamarin da ya jawo tsaiko wajen tabbatar da shi a majalisar, musamman bayan majalisar tattalin arzikin ƙasar ta buƙaci a dakata.

Sai dai a makon jiya ne ƙungiyar gwamnonin ƙasar ta amince da ƙudurin, amma tare da yin wasu kwaskwarima da ta ce zai magance abubuwan da ake fargaba.

Da yake jawabi a wajen wani taro mai taken The Platform, Oyedele ya ce za a fara amfani da dokar ne a watan Yulin bana.

An bukaci EFCC ta gurfanar da jami’an ta 27 da ta kora daga aiki a gaban kotu.

NAHCON ta sanar da kuɗin aikin hajjin 2025 a Najeriya

“Muna sa ran za a amince da ƙudurorin haraji kafin ƙarshen rubu’i na farko na wannan shekarar, inda za mu ba masu biyan haraji lokaci domin su fara shiri kafin ya fara aiki a watan Yuli,” in ji shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya kamata INEC ta daina gudanar da zaɓen cike gurbi idan ɗan majalisa ya mutu ko ya ajiye aikin sa – a cewar Falana

A game da cire tallafin man fetur, Oyedele ya ce yana cikin manyan matakai masu muhimmanci da aka ɗauka a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button