
Ƙasar Italiya ta naɗa tsohon ɗan wasanta Gennaro Gattuso a matsayin sabon kocin da zai jagoranci ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar.
Gattuso wanda tsohon tauraron ƙungiyar ƙwallon ƙafa na AC Milan ne, ya maye gurbin Luciano Spalletti, wanda aka bayyana sallamar sa daga aiki a yayin taron manema labarai a makon da ya gabata.
Gattuso mai shekara 47 ya buga wa ƙasar Italiya wasannin 73 a matsayin ɗanwasa kuma yana cikin ayarin ƙungiyar da tayi nasarar lashe gasar Kofin Duniya ta 2006.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Italiya ta ce za ta gabatar da Gattuso ga ‘yan jarida a ranar Alhamis.









