
Kazim Abiola, yayi nasarar kasancewa Alkalin wasa na farko daga Najeriya da zai yi alkalanci a gasar cin kofin kasashen nahiyar Afrika na zallan yan’wasan dake taka leda a gida da kasashen Kenya da Uganda da kuma Tanzania zasu karbi bakuncin sa.
Wannan dai shine karon farko da hukumar ta CAF za ta fara amfani da Alkalin wasa daga Najeriya a irin wannan gasa.
Hukumar ta CAF ta fidda jerin sunayen alkalan wasa 26 da zasu jagoranci tafiyar da wasannin da za’a fafata daga ranar 1 zuwa 28 ga watan Fabrairu da ke tafe.









