Labarai

Firaministan Indiya ya isa Amurka don ganawa da Trump

Firaministan Indiya Narendra Modi ya isa Washintong domin ganawa da Donald Trump yayin da ake tsaka da nuna damuwa kan haraje-harajen da Amurka ke ƙaƙabawa da kuma batun baƙin haure.

Ana tunanin cewa Mista Modi na iya rage wasu shingen kasuwanci kan muhimman kayayyakin da Amurka ke shigowa da su domin daƙile duk wani ƙarin harajin da za a iya sanyawa.

Ana kuma sa ran Shugaba Trump zai nemi Delhi ta kwashe ‘yan ƙasarta da ba su da takardun izinin zama Amurka.

Wasu alƙaluma sun ce kusan Indiyawa 700,000 ne ke Amurka ba bisa ƙa’ida ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button