Labarai

Ana samun ci gaba a tattaunawar tsagaita wutar yaƙin Gaza a Masar

Rahotonni daga birnin Alqahira na cewa ana samun ci gaba a tattaunawa tsagaita wutar yaƙin Gaza da ake gudanar da birnin.

Jami’an Masar sun gana da wakilan Hamas, wadda ta yi barazanar dakatar da sakin Isra’ilawan da aka tsara za ta saki kan abin ta da kira ”saɓa wa yarjejeniyar”.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa za a koma mummunan faɗa idan Hamas ta ƙi mayar da wadanfda take garkuwa da su a ranar Asabar ba.

Masu sanya idanu kan yarjejeniyar zaman lafiyar sun ce motocin kayan agaji masu yawa sun shiga Gaza tun bayan fara aiwatar da yarjejeniyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button