LabaraiWasanni

Iyalan Michael Oliver na fuskantar barazana daga magoya bayan Arsenal

Iyalan shahararren alhakin wasan nan na kasar Ingila, Michael Oliver na cigaba da samun kulawar jami’an tsaro biyo bayan kalaman suka da Michael Oliver ke fuskanta daga magoya bayan kungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal bisa jan kati da ya bawa ɗan wasan bayan kungiyar, back Myles Lewis-Skelly bisa a wasan da Arsenal ta fafata da Wolves.

Tuni dai Arsenal tayi nasara akan ɗaukaka karar da tayi akan dakatawar da akayi wa dan wasan na ta, sai dai kuma Michael Oliver ya cigaba da fuskantar barazana daga magoya bayan kungiyar ta Arsenal.

Sai dai kuma tsohon ɗan wasan ƙwallon kafa na kasar Ingila, Gary Neville, wanda ya bayyana Michael Oliver ƙwararren alkalin wasa da kasar Ingila ke alfahari dashi, ya bayyana rashin gamsuwa da irin kalaman da kocin Arsenal Mikel Arteta ya furta akan lamarin, yana mai cewa kalaman na Arteta sun taka rawa tare da karfafa sukar da magoya bayan Arsenal din kiyi akan kuskure da a cewar Michael Oliver yayi wanda a matsayin na alkalin wasa ya kamata a yi masa uzuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button