LabaraiLafiya

Matar Ekweremadu ta koma Najeriya bayan kamalla zaman gidan gyaran hali a Burtaniya

Matar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu, Madam Beatrice Ekweremadu, ta koma Najeriya bayan sakinta daga kurkuku a Birtaniya.

A watan Maris na 2023 ne kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan jikin ɗan adam ta hanyar ɗauko wani ɗan matashin daga Najeriya mai shekara 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa ‘yar su.

Kotun ta kuma sami wani likita mai shekara 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da ɗan siyasar wajen samo mutumin da zaa cire wa ƙodar.

A lokacin kotun ta yanke wa tsohon shugaban majalisar dattawan ɗaurin shekara 10.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button