LabaraiSiyasa

2027 za ta zo da ban mamaki – inji Rabiu Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar shugabancin kasa a zaɓen shekara ta 2023 a inuwar jam’iyyar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya jan hankali yan Najeriya dasu lura da kyau, su kuma buɗe idanun su tare da amfani da hankula su domin kaucewa fadawa tarkon yan siyasar babbar riga.

Kwankwaso wanda ya bayyana haka a yayin hira da jaridar Punch, ya kara da cewa yan siyasa da dama a yanzu sun baza hajjar yaudarar al’umma domin neman samun goyon baya.

Jagoran na jam’iyyar NNPP, ya kuma bayyana cewa duk da cewa jam’iyya mai mulkin Najeriya APC na nunawa yan ƙasar cewar a cikin ta babu baraka amma lokaci shine zai tabbatar da hakan, domin kuwa dukkanin alamu sun nuna cewa akwai tarin matsaloli a tsakanin mambobin jam’iyyar har ma da wasu daga cikin jami’in gwamnati, lamarin da ya ce, ya samu asali ne daga rashin cika alƙawari na buƙatu irin na siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button