
Mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ƙasar Brazil, Carlos Ancelotti ya bayyana dalilan da ya sa ba’a ga sunayen fitattun yan wasan ƙasar biyu ba cikin jerin sunayen yan wasa da zasu wakilci Brazil a wasan neman gurbin cin kofin duniya da za’a gabatar a wata mai zuwa.
A jiya Litinin ne, Ancelotti ya fitar da jerin sunaye yan wasa 26 da zasu wakilci Brazil a wasan da za tayi da Chile da kuma Bolivia a wata mai zuwa, sai dai kuma babu sunayen Neymar wanda ke wasa a Santos da kuma ɗan ƙungiyar Real Madrid, Rodrygo a cikin jerin sunayen da ya fitar.
Sai dai kuma an ga sunayen sabbin yan wasa da suka hada da Kaio Jorge da Caio Henrique da Douglas Santos da João Pedro da kuma Luiz Henrique.
Da aka yi masa tambaya akan dalilan da suka sa bai gayyaci yan wasan biyu ba, Ancelotti ya bayyana cewa akwai sharudda da ya kamata dan wasa ya cika kafin ya samu gayyatar zuwa wakiltar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta kasa, kuma yan wasan biyu basu cika wannan sharuddan ba, musamman ma kasancewa cikin kyakkyawan yanayin iya yin wasa.









