LabaraiWasanni

Hukumar gudanarwar gasar Laliga ta ƙi amincewa da buƙatar Madrid na matso ma ta da wasan Alaves.

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta gabatar da bukata ga hukumar shirya gasar Laliga kan a matso ma ta da wasan da za ta fafata da Alaves daga ranar Lahadi zuwa Asabar domin bawa yan wasan ta damar kara samun hutu kafin wasan ta da Arsenal.

Sai dai kuma duk da cewar Real Madrid ta samu amincewar abokiyar karawar ta Deportivo Alaves kafin gabatar da bukatar, hukumar gasar ta Laliga ta ƙi amincewa da wannan hakan abinda ke nuni da cewar wasan yana nan a ranar Lahadi kamar yadda aka shirya shi tun da farko.

Real Madrid dai za ta fafata wasan mako na 31 ‘na gasar Laliga da Deportivo Alaves a ranar Lahadi, sannan kuma ta karbi bakuncin Arsenal a wasan zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a ranar Laraba, wasan da a zagaye farko tayi rashin nasara da ci uku da nema.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button