Labarai
An ci tarar wani mutum sama da naira 300,000 saboda saka waya a sifika.

An ci tarar wani mutum euro 200, wato sama da naira 300,000 saboda saka waya a sifika lokacin da yake waya a wata tashar jirgin ƙasa da ke Faransa – ya ƙalubanaci tarar.
Mutumin mai suna David, ya shaida wa kafar talibijin ta Faransa mai suna BFM cewa yana waya ne da ƴar’uwarsa a tashar Nantes ranar Lahadi a lokacin da wani jami’i daga kamfanin jirgin ƙasan, SNCF, ya tunkaro shi.
David ya ce jam’in ya ce za a ci tarar sa euro 150 idan bai kashe sifikar ba – tarar da yayi iƙirarin daga bisani an ƙara ta zuwa euro 200 saboda bai biya kuɗin nan take ba.
Tuni dai ya ɗauko lauya domin ƙalubalantar tarar.
Kamfanin SNCF ya tabbatar da cewa jami’in tsaronsu ne ya ci tarar David a wani wuri da babu hayaniya.









