Labarai

Jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga kan layin dogo

Jirgin ƙasa ɗauke da fasinja da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga layin dogo hana tsaka da tafiya.

Lamarin dai ya jefa fargaba a tsakanin fasinjoji da ke cikin jirgin.

A cewar rahotanni lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a kauyen Asham da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna kuma jirgin ƙasa ya taso daga Abuja ne da misalin karfe 9:45 na safiyar talata.

Har yanzu ba a san sababbin dalilin da ya jawo saukar jirgin daga kan layin dogo ba, kuma babu tabbacin ko an samu waɗanda suka jikkata.

Hukumar Jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC) ba ta yi tsokaci a kan lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button