
Mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ƙasar Najeriya, Eric Chelle, ya tabbatar da cewa dukkanin yan wasan Super Eagles na cikin koshin lafiya, kuma sun shirya tsaf domin samun nasara a wasan da ƙungiyar za ta fafata da Zimbabwe da yammacin yau Talata.
Eric Chelle wanda ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da manema labarai, ya kuma yi hasashen cewa duk da cewar wasan ƙwallon ƙafa bashi da tabbas, amma yana da tabbacin cewar a karshen wasan Najeriya za tayi nasara samun maki ukun da ya dace da ita.
“Mun kamalla dukkanin shirye-shiryen da ya dace, kuma na tattauna dukkanin yan wasan mu akan tsarin da zamu yi amfani dashi a yayin wasa don ganin mun samu nasara” a cewar Eric Chelle.
Da yake karin haske, mai rikon mukamin kaftin ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, William Troost Ekong, ya bayyana cewa tun bayan kamalla wasan da suka doke ƙasar Rwanda da ci biyu da nema, yan’wasan suka maida hankali wajen fuskantar wasa da zasu fafata da Zimbabwe.
“Ina tabbatar wa da yan Najeriya cewa a shirye muke mu fuskanci Zimbabwe, abinda kawai muke bukata daga gare su shine goyon baya da kuma addu’ar samun nasara'” a cewar William Troost Ekong.
Najeriya dai za ta fafata da kasar Zimbabwe a wasan sharar fagen neman kaiwa ga shiga gasar cin kofin duniya na nahiyar Afrika, a inda Najeriya ke a matsayi na na hudu a rukunin ‘c’ wanda ya kunshi kasashen da suka hada da Afrika ta Kudu da Lesotho da Rwanda da Benin da Zimbabwe da kuma Najeriya.
Za dai a gabatar da wasan ne a filin wasa na Godswin Akpabio dake Uyo, a jihar Akwa Ibom da misali karfe biyar na yammacin Talata.









