Labarai
Tsananin sanyi ya sa za a yi bikin rantsar da Trump a cikin ɗakiDonald Trump

Za a mayar da bikin rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka – wanda za a yi a ranar Litinin – zuwa cikin wani ɗakin taro.
An kwashe makonni ana shirya yadda za a yi bikin a farfajiyar Majalisar Dokokin Amurka ta Capitol da ke birnin Washington, sai dai a yanzu an yanke shawarar yin bikin a ƙarƙashin gubbar Majalisar.
Wannan sauyi na nufin mutane ƙalilan ne za su samu halartar wurin rantsuwar.
Sai dai Donald Trump ya ce za a haska kai-tsaye yadda rantsuwar za ta gudana a wani katafaren ɗakin taro da ke maƙwaftaka da majalisar.
Ronald Reagan ne shugaban ƙasa na ƙarshe da aka yi bikin rantsar da shi a cikin ɗakin taro, lokacin da ya sha rantsuwar wa’adin mulkinsa na biyu, a shekarar 1985









