
Dan takarar jam’iyyar Labour Party a zaɓen da ya gabata, Peter Obi, yayi kira ga Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu kan ya dinga nuna kishi kasa a al’amurran sa na rayuwa, ganin cewar a yanzu fa Najeriya ya ke shugaban ta ba wai jihar Legas ba.
A cewar Peter Obi, kamata yayi Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya kasance yana gabatar da bukukuwa sa a sassa daban-daban na Najeriya a matsayin sa na shugaba, ba wai a jihar Legas kaɗai ba.
“Kamata yayi mu ga shugaban Najeriya ya halarci bikin Sallah a Sokoto ko kuma bikin Kirsimeti a Anambra, wannan shine zai kara kyautata hadin kai da cigaban ƙasa, inji Peter Obi”.
Da ya juya kan gyaran dokar zaɓe, dan takarar na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya bayyana aikin a matsayin babban kalubale da zai kai ga samun zaɓen da al’ummar kasa zasu aminci dashi.
Daga karshe, Peter Obi, ya sharwarci shugabannin a matakai daban-daban dasu kyautata alaƙar su da wadanda suke wa jagoranci, yana mai cewa yin hakan zai taimaka wajen ganin an samu fahimtar juna tsakanin mai mulki da wadanda ake mulka.









