LabaraiWasanni

Ɗan Wasa Diogo Jota Ya Rasu Sakamakon Hatsarin Mota

Dan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool kuma ɗan ƙasar Portugal, Diogo Jota, ya rasu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a yankin Zamora da ke ƙasar Spaniya.

Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya afku ne bayan tayar motar ƙirar Lamborghini da yake ciki ta fashe, lamarin da ya haifar da kamawar motar da wuta.

Hatsarin ya yi sanadin mutuwar Diogo Jota tare da kanensa, Andre Felipe, wanda shi ma ke cikin motar a lokacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button