An rufe ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya.

A yau Alhamis, Ƙasar Amurka ta rufe ofishin jakadancin da ke babban birnin tarayya Abuja da kuma jihar Legas na ɗan takaitaccen lokaci domin nuna alhini kan rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Jimmy Carter wanda ya rasu a ranar 29 ga watan Disamba shekarar da ta gabata.
A wani sako da ta wallafa a shafi ta na X, ofishin jakadancin na Amurka ta bayyana Jimmy Carter a matsayin jajirttaccen shugaba da ya sadaukar da rayuwar wajen karfafa zaman lafiya da tabbatar da mulkin demokradiyya a fadin duniya da kuma yancin ɗan adam.
Spain Super Cup: Real Madrid za ta fuskanci turjiya daga Mallorca.
Anyi ganawar sirri tsakanin Shugaban Najeriya da ministan harkokin wajen kasar China.
Tsohon shugaban na kasar Amurka, Jimmy Carter ya rasu yana da shekaru dari a duniya.









