Labarai

Alƙali ya yanke wa Trump hukuncin sallama ba tare da wani sharaɗi ba.

Alƙalin da ke yi wa zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump shari’a kan ba da toshiyar baki ga wata ‘yar fim ɗin batsa ya yanke masa hukunci.

Mai Shari’a Juan Merchan ya yanke masa hukuncin sallama ba tare da wani sharaɗi ba a kan duka tuhuma 34 da ake yi masa.

Merchan ya faɗa wa kotun cewa ya fahimci sallamar Trump ita ce “hukunci ɗaya kacal da ya dace da doka ba tare da an ci mutuncin ofis mafi girma a ƙasar Amurka ba.

Hukuncin na nufin Trump ba zai biya wata tara ba, ko zaman gidan yari duk da kama shi da laifi a duka tuhuma 34 da ake yi masa game da yin ƙarya a bayanan harkokin kasuwancinsa.

Duk da haka Trump ya ce zai ɗaukaka ƙara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button