Ana fargabar samun ƙarancin Man Fetur a Najeriya.

Wata taƙaddama tsakanin ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas na Najeriya NUPENG da kuma kamfanin matatan man ta Dangote, na neman jefa haifar da ƙarancin man fetur a fadin Najeriya.
A wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas a Najeriya, Williams Akporeha, da kuma sakataren ƙungiyar na kasa, Afolabi Olawale, ta zargi kamfanin matatan mai ta Dangote da hana deribobin sabbin motocin da ta sayi masu amfani da iskar gas na CNG kimanin 10,000 zama mambobin ƙungiyar, abinda ta ce ya sabawa dokar kwadago ta kasa da kuma sashi na ƙundin tsarin mulki Najeriya.
A don haka ƙungiyar tayi kira ga mambobin ta da ke aikin a matatan man dasu kauracewa wuraren aikin tare da daina daƙon mai daga ranar Litinin mai zuwa.









