KasuwanciLabaraiTattalin Arziki
2026: Sai da lambar shaidar biyan haraji za’a bude asusun banki a Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Janairun shekara mai zuwa, wajibi ne ga dukkanin mai don bude asusun banki a Najeriya ya zamanto ya mallaki lambar shaidar biyan haraji.
Wannan dai na daya daga cikin tanadin dokar haraji da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya sanya wa hannu da zata fara aiki a farkon shekara mai zuwa.
A cewar tanadin dokar wajibi ne ga dukkanin dan kasa wanda shekarun da suka kai ga biyan haraji da ya mallaki wannan lambar.
Haka kuma abin ya ke ga hukumomi da ma’aikatun gwamnati na ƙanana hukumomi, ko na jiha da kuma na gwamnatin tarayya.









