LabaraiWasanni

DA ALAMA JOSHUA ZIRKZEE ZAI BAR MANCHESTER UNITED ZUWA JUVENTUS

Rahotanni daga kasuwar musayar yan’wasa sun bayyana cewa shirye-shirye sun yi nesa a kokarin da ɗan wasan Manchester United, Joshua Zirkzee, ke yi na barin ƙungiyar a matsayin aro zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus.

Joshua Zirkzee, mai shekaru 23 a duniya, na cigaba da fuskantar kalubale a sa a Manchester United, tun bayan musayar sa da ƙungiyar tayi daga Bologna akan kuɗi Dala miliyan 42.

A cewar jaridar Gazzette, Juventus wacce a yanzu haka ke karkashin mai horar wa, Thiago Motta, wanda a baya shine kocin Thiago Motta a Bologna na duba yiyuwar daukar ɗan wasan a matsayin aro zuwa karshen kakar wasannin da muke ciki.

Sai dai har zuwa yanzu ba’a cimma yarjejeniyar ba tsakanin ƙungiyoyin biyu.

Shin ku na ganin ya kamata Joshua Zirkzee ya bar Manchester United zuwa Juventus?

Ku bayyana mana ra’ayin ku a comment section na wannan labarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button