
Hukumar da ke shirya gasar zaɓen gwarzon ɗan wasan ƙwallon kafa na shekara-shekara, da ake wa lakabi da Ballon d’Or ta bayyana ranar da za’a gudanar da bikin bayar da kyautar na wannan shekarar.
Kamar yadda ya ke a ƙunshi a bayanan da hukumar ta fitar, a ranar 7 ga watan Agusta, ita ce ranar da hukumar za ta bayyana sunayen yan wasa da zaa fidda gwani-na-gwanayen daga cikin su a fannin ƙwallon ƙafa ta maza da ta mata da gwarzon matashin ƙwallon ƙafa na duniya, da kuma zaɓen mai tsaron ragar da yafi bajinta na shekarar 2025 a fannin maza da kuma mata.
Za’a dai gudanar da bikin na wannan shekarar ne a ranar 22 ga watan Satumba a birnin Paris.









