KasuwanciLabaraiTattalin Arziki

Shin ko ka san Ƙasashe da kuɗin Najeriya ya fi nasu daraja, ga biyar daga ciki..

Duk da lalacewar darajar kuɗin Naira da ake amfani da ita a Najeriya, akwai kuɗin ƙasashen da Naira tafi daraja.

Ga biyar daga cikin ƙasashen da Naira Najeriya tafi kudin da ake amfani dasu a can daraja!

Vietnam
Ƙasa ta farko da Naira Najeriya tafi fifikon daraja ita ce Vietnam, a inda ake canjar da Naira Najeriya daya akan sama da kuɗin Vietnamese Dong 16.

Indonesiya
Kasa ta biyu ita ce Indonesia, a inda Naira daya ta Najeriya ta ke daidai da Rupiah 10 na kuɗin Indonesia.

Uganda
Baya ga Indonesiya, kasa ta uku da Naira Najeriya ke da daraja fiye da kuɗin kasar, ita ce Shillings da ake amfani da ita Uganda, a inda darajar Naira daya ta Najeriya ta ke akan Shillings na Uganda 2.45.

Tanzania
Tanzania ita ce kasa ta hudu da darajar kuɗin ƙasar watau Tanzania Shillings ya ke kasa da Naira ta Najeriya. Ana dai canjar da Naira akan Tanzania Shillings 1.71.

Lebanon
Ƙasa ta biyar da Naira Najeriya ta fi kuɗin ƙasar daraja ita ce ƙasar Lebanon, a inda ake canjar da Naira daya ta Najeriya akan Fam 59.80 na Lebanon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button