
A ranar Lahadi za’a gabatar da wasannin mako na 33 na gasar ƙwallon ƙafa shin ƙwararru na kasa.
A filin wasa na Kofar Mata da ke Kano, Kano Pillars za ta karbi bakuncin Lobi Stars, yayin da Heartland za ta ziyarci Enugu Rangers.
A Akure, Sunshine Stars na gida ita da Enyimba yayin da Plateau United ke ziyartar Nassarawa United, sai kuma wasa tsakanin Remo Stars da Katsina United.
Sauran wasannin gasar da za’a fafata sun hada da wasa tsakanin Abia Warriors da Rivers United yayin da El-Kanemi Warriors za ta ziyarci Akwa United, sai kuma Ikorodu City da zata karbi bakuncin Niger Tornadoes yayin a Ilorin, Kwara United ke kasancewa a gida domin karawa da Bendel Insurance.
Zuwa yanzu dai Remo Stars ita ce akan gaba da yawan maki 61, yayin da River’s United ke biye ma ta baya a matsayi na biyu da maki 55, sai Abia Warriors a matsayi na uku da maki 50 yayin da Ikorodu City ke a matsayi na hudu da maki 49.
Babban abin tambaya shine, shin me ya jawo koma-bayan da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da suka fito daga arewacin ƙasar nan suke fuskanta a wannan kakar?









