LabaraiWasanni

Fafatawa da Manchester United zai zama abin alfahari – De Gea

Tsohon mai tsaron ragar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United David de Gea, ya bayyana fatan samun nasara a karawar da ƙungiyar sa ta Fiorentina za tayi da tsohuwar Manchester United a wasan sada zumunci.

A cewar David de Gea, fuskantar Manchester United a wasa, lamari ne na musamman a gare shi, kuma yana farin ciki da yin hakan tare da fatan samun nasara.

Wannan dai shine karon farko da David de Gea zai fuskanci tsohuwar kungiyar ta sa tun bayan barin sa ƙungiyar a karshen kakar wasannin shekarar ta 2023, za kuma a gabatar da wasan sada zumuncin ne a tsakanin ƙungiyoyin biyu a ranar Asabar tara ga watan gobe na Augusta a filin wasa na Old Trafford.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button