LabaraiWasanni

Salah ya ƙalubalanci UEFA akan mutuwar Suleiman Al-Obeid a Gaza.

Dan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, ya bukaci hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar turai da ta fito fili ta bayyana musabbabin mutuwar dan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar Falasɗinu, Suleiman Al-Obeid, wanda rohotanni suka ce ya rasa ransa a lokacin da yake kokarin karbar wa iyalan sa abincin yan gudun hijira a zirin Gaza.

Mohammad Salah wanda ya bayyana rashin jin dadin sa da salon ta’aziya da hukumar ta UEFA tayi akan Marigayin, wanda yayi fice a wasan ƙwallon ƙafa da har ake masa lakabi da Pelen Falasɗinawa, ya nemi hukumar ta bayyana dalilan da yayi sanadiyar rasa ran ɗan wasan da yadda ya rasu da kuma wurin da lamarin ya faru, yana mai cewa yin hakan shine zai bayyana irin halin da mazauna zirin Gaza ke ciki na tsawon lokaci.

Suleiman Al-Obeid wanda ke da shekaru 41 a duniya yayi wasa a ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama a yankin Gaza kuma ya kasance daya daga cikin yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Falasɗin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button