Kotun ɗaukaka kara ta tabbatar da hukuncin da ya ayyana ƙungiyar IPOB a matsayin ƙungiyar yan ta’adda

Kotun ɗaukaka kara da ke zaman ta a Abuja ta amince da hukunci babban kotun tarayya dake Abuja ta yi ns ayyana ƙungiyar IPOB a matsayin ƙungiyar yan’ ta’adda kuma haramtacciya.
A wani hukunci na bai-daya da alkalan kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a, Hamma Barka, suka yanke, sun bayyana cewa babu wasu hujjoji da zai sa kotun ta sauya hukuncin na babbar kotun tarayya ta yanke tun da farko da ayyana ƙungiyar ta IPOB a matsayin haramtacciya a kasar nan.
A cewar kotun, gwamnatin tarayya ta bi dukkanin matakan da suka dace wajen samun hukuncin kotun, bisa la’akari da yadda ayyukan ƙungiyar je zama barazana ga rayuwa da dukiyoyin al’ummar Najeriya.
A ranar 15 ga watan Satumba shekara ta 2017, alkalin babban kotun tarayya na wancan lokaci, Marigayi mai Shari’a Abdul Abdu-Kafarati ya yanke hukuncin da ya haramta kungiyar ta IPOB tare da ayyana ta a matsayin ƙungiyar yan’ ta’adda biyo bayan bukatar yin hakan da Ministan Shari’a na wancan lokacin Abubakar Malami ya gabatar a madadin gwamnatin tarayya.









